Ana zaman dar dar a jihar Jigawa

A garin Hadeja dake jihar Jigawa a Arewacin Najeriya ana zaman dar dar tsakanin 'yan shi'a da shugabannin babban masallacin juma'a dake kofar fadar sarkin garin wadanda 'yan shi'ar ke dangantasu da kungiyar Izala.

Wannan sabanin dai yana faruwa ne sakamakon wa'azi ko fadakarwar da su 'yan shi'ar ke ikirarin cewa suna gudanarwa a duk ranar juma'a.

Tuni dai kwamishinan 'yan sandan jihar ta Jigawa ya gudanar da wani taro da bangarorin biyu da sauran jami'an gwamnati da ke da nasaba da lamarin domin samun maslaha.