Ma'aikata a Girka sun fara yajin aiki

Ma'aikata suna bore ne domin nuna amincewa da matakan gwamnati
Image caption Dubun dubatar ma'aikatan kasar ne shirin zai shafa

A yau za'a fara wani yaji aikin gama gari a kasar Girka domin nuna rashin amincewa kan tsauraran matakan da gwammatin kasar ta kafa karkashin shirin kasashen duniya na ceto kasar daga komabaya a tatalin arziki.

Dubun dubatar ma'aikatan gwamnati wadanda shirin zai fi shafa zasu gudanar da zanga zangar a birnin Athens.

Bugu da kari dubanin jami'an tsaro masu kwantar da tarzoma zasu kasance a bakin aiki bayan da zanga zangar da aka gudunar a kwanakin baya ta janyo tashe tashen hankula.

Asusun bada lamuni da kuma kasashen dake turai, sun ba kasar ta Girka biliyoyin daloli domin taimakama kasar ta fito daga matsalar tababarewa a tattalin arzki, abun da kuma ya sa gwamnatin kasar ta tsuke bakin aljihunta.