Abba Abacha ya daukaka kara a Switzerland

Tutar Sitzerland
Image caption Switzerland ta maidawa Najeriya kudaden da marigayi Abacha ya ajiye a kasar

Wata kotun daukaka kara a Switzerland na sauraran karan da dan tshohon shugaban sojin Najeriya marigayi Janar Sani Abacha ya gabatar a gabanta wanda yake kalubalantar hukuncin da wata kotun a kasar ta yanke mai na maida wasu kudadae da yawansu ya kai dala miliyan dari uku da hamsin.

Kotun dai ta kama Abba Abacha dan marigayin da laifin kasancewa cikin wata kungiyar masu aikata laiffuka.

Kotun majistaren ta birnin Geneva ta yankewa Abba Sani Abacha hukunci ne cikin watan Nuwamban bara.

Lauyoyin Abba Abacha dai sun ce ba zai samu damar halarta zaman kotu ba, saboda yana Najeriya.

Marigayi Janar Sani Abacha ya rasu ne a kan karagar mulki a shekara 1998, kuma bayan rasuwarsa, kasar Switzerland ta mayar wa Najeriya wasu kudade da marigayin ya ajiye a wasu bakuna a kasar.