Tarrayar Turai za ta kafa gidauniya

Alamar kudin Euro na Tarrayar Turai
Image caption Alamar kudin Euro na Tarrayar Turai

Ministocin kudi na Kungiyar Tarayyar Turai sun amince da kafa wani asusu na sama da dala biliyan dari shida don tallafawa tattalin arzikin kasashen da ke amfani da kudin bai-daya na euro.

Ministocin sun bayyana cimma wannan yarjejeniya ne bayan wani taro da suka shafe sa'o'i goma sha daya suna yi a birnin Brussels.

Ba a dai zaci taron zai haura sa'o'i biyu ba; amma da muhawara ta yi muhawara sai da ya kai ministocin tsakar dare.

A karshe dai an cimma matsaya, bayan makwanni ana fargabar matsalar bashin da ta mamayi kasar Girka za ta iya bazuwa zuwa wasu kasashen masu amfani da kudin euro.

Hanyoyin samo kudaden

Manufar wannan tallafi dai ita ce tabattarwa kasuwannin hada-hadar kudade cewa ba za a bari kasashen da ke fama da matsalar bashi, da ma wadanda ke da rangwamen karfin tattalin arziki, su shiga halin ha'ula'i ba.

Kwamishinan harkokin kudi na Kungiyar Tarayyar Turan, Ollie Rehn, ya bayyana cewa wannan yarjejeniyar tana nuni ne da cewa kasashen Turai za su yi duk abin da ya kama don ganin sun bayar da kariya ga kudin euro.

Ya kuma ce Asusun Bayar da Lamuni na Duniya, wato IMF, zai bayar da rabin kudaden da Tarayyar Turan za ta bayar.

“Bayan wata ganawa da [muka yi da] Asusun Bayar da Lamuni na Duniya, da kuma shugaban asusun, Dominique Strauss-Kahn, asusun na IMF ya amince ya taka rawa ta hanyar samar da rabin kudaden da Tarayyar Turai za ta samarwa asusun namu”, inji Mista Rehn.

Rawar da Bankin Turai zai taka

Babban Bankin Tarayyar Turai ya tabbatar da cewa a karo na farko a shirye yake ya dauki nauyin biyan basussukan da ake bin gwamnatocin kasashen na Turai.

Tuni dai darajar kasuwannin hada-hadar kudade a nahiyar Asiya ta fara yin sama sakamakon wannan gagarumin tallafin na Tarayyar Turai.

Rahotanni sun ce bayan sanarwar, darajar kudin euro ta karu, sannan darajar hannayen jari ta yi sama a kasuwannin na Asiya.