Shekarau ya marawa Takai baya

Taswirar Najeriya
Image caption Ana ci gaba da samun badakala a harkar siyasan Najeriya

Gwamnan Jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana dalilan da suka sa ya fito fili ya nuna wanda ya ke so ya gaje shi a zaben badi.

A makon da ya gabata ne dai gwamnan ya bayyana Alhaji Salihu Sagir Takai a matsayin wanda yake so ya gaje shi a matsayin gwamnan jihar.

Wannan furuci ya janyo suka daga wadansu magoya bayan jam’iyyar ANPP mai mulkin jihar, ya kuma shammaci wasu 'yan jam'iyyar da dama.

Malam Shekarau ya shaidawa BBC cewa ya yi hakan ne saboda burin da ya ke da shi na ganin bayansa ta yi kyau.

Tsaka mai wuya

“Ko ban fadi dalili ba”, inji gwamnan, “za a iya kyautata min zato….

“Ba wanda ba ya son bayansa ta yi kyau; ba wanda baya son ya waiwaya baya ya ga cewa dansa ya gaje shi, ya ma taka rawa fiye da shi".

Gwamnan ya kara da cewa kasancewar ya yi shekaru a gadon mulki, “in har akwai wasu alkaluma da ya kamata wani ya sani na me ake nema ne a wajen wanda zai yi gwamna, ina ganin yanzu sai dai in karantar da wasu”.

Sai dai kuma wasu na ganin cewa wannan mataki ka iya jefa jam’iyyar ta ANPP cikin halin tsaka mai wuya a jihar ta Kano.

Batun magada na daukar hankali

Amma Malam Shekarau ya ce masu fadar hakan masu suka ne wadanda ko ma wa aka dauka sai sun yi sukar.

“Duk fa kwaramniyar nan magana ce ta masu shiga rediyo da jaridu ana rubuce-rubuce.

“Babu wanda ya je ya yi aiki da wasu alkaluma da za a zo da su a bayyane—illa mutane na bayyana ra’ayinsu, kuma mun ce wannan dimokuradiyya muke yi”.

Yayin da ake shirye-shiryen tunkarar zabubbukan shekarar 2011 dai, batun wadanda za su gaji gwamnonin da wa'adin mulkinsu ke cika a karo na biyu shi ne abin da ke jan hankulan jama’a a wadansu jihohi na Najeriya.