Matsalar karancin wutar lantarki ta addabi jihar Borno

Mutane na fama da rashin wutan lantarki
Image caption Rashin isashen wutan lantarki yasa sana'o'i da dama sun durkushe

A jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya, jama'a kan shafe kwana da kwanaki ba su ga hasken wutar lantarkin ba.

Wata babbar matsalar ma itace ta tsananin zafin da ake fuskanta a jihar wanda rashin wutar lantarkin ya dada jefa jama'a cikin halin kunci.

Gwamnatin jihar Bornon tayi wata ganawa tare da manyan jami'an Kamfanin Samar da Wutar Lantarkin ta kasa domin nemo hanyoyin da za'a saukaka wannan matsala da ta addabi jama'ar jihar.

Ta kuma ce ta gano bakin zaren, kuma nan bada jimawa ba, za'a shawo kan matsalar.