Mutane biyu sun halaka a jihar Kano sanadiyar guguwa

Guguwar ta raunaka mutane da dama
Image caption Guguwar ta raunaka mutane da dama

A jihar Kano dake arewacin Najeriya, wata iska mai karfi tare da ruwan sama ta yi sanadiyyar rasuwar mutane akalla biyu da raunata wasu, tare da rushewar sama da gidaje dari.

Wannan lamari dai ya faru ne a daren ranar Lahadi, a Unguwannin Bachirawa da kuma kauyen Kunture dukkansu a karamar hukumar Ungoggo.

Iskar ta kuma yi sanadiyyar karyewar turakun wayoyin wutar lantarki, wato Pole wire.

Sai dai har zuwa yanzu jama'ar yankin sun shedawa BBC cewa babu wani tallafi da suka samu daga hukumomi sakamakon wannan bala'i da ya afka musu