Jamiyyar Liberal Democrats za ta yanke shawara a yau

Shugabanin manya Jamiyyun Burtaniya
Image caption Jamiyyar Liberal democrats na nema jamiyyar da za ta cimma bukatunta

Jamiyyar Liberal Democrats a Birtaniya ta bayyana cewa idan an jima a yau talata ne za ta bayyana jamiyya daya daga cikin jamiyyun Labour da na Conservatives wadda za ta hada kai da ita domin kafa gwamnati.

Jamiyyar ta gudanar da tattaunawarta ta farko a hukumance tare da jamiyyar Labour bayanda shugabanta, kuma Piraministan kasar Gordon Brown ya bayyana aniyarsa ta sauka daga mukaminsa cikin watanni masu zuwa.

Wakilin BBC ya ce Gordon Brown yayi karfin hali, ba kawai don tabbatar da jamiyyar Labour akan karagar mulki ba, har ma da sauya fasalin siyasar Birtaniya, ta hanyar hadin gwiwar da ba a taba ganin irinsa ba tun bayan yakin duniya na biyu.