Kungiyoyin kwadago sun fara tsokaci kan rahoton ILO

Taswirar kungiyar ILO
Image caption ILO itace kungiyar kwadago ta duniya

A Jamhuriyar Niger, wasu kungiyoyin kare hakkin jama'a da kuma na yaki da ci-da-gumin yara sun fara tsokaci game da sakamakon wani rahoto da kungiyar kwadago ta duniya, ILO, ta fitar.

Rahoton, wanda aka fitar jiya a kasar Holland, a lokacin taron kasashe akan matsalar ayyukan da kananan yara ke yi, ya nuna ana samun karuwar jefa yara 'yan kasa da shekaru sha hudu cikin ayyukan karfi.

A cewar rahoton, matsalar ta fi kamari a kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara, ciki har da Nijar.

A kasar ta Nijar an fi danganta matsalar da wuraren aikin hakar ma'adinai ko almajirci.