Spain ta dau mataki kan tattalin arziki

Firayim Ministan Spaniya, Zapatero
Image caption Hukumar Turai ta yi kira ga Spaniya da ta tsuke aljihunta

A yau ake sa ran Firayim Ministan Spaniya zai gabatar da jawabi kan yadda gwamnatin kasar za ta shawo kan matsalar gibin kasafin kudin kasar.

Sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da ake fargabar cewa matsalar bashi da kasar Girka ke fuskanta ka iya yaduwa zuwa sauran tattalin arzikin kasasahen duniya masu rauni.

Hukumar turai ta yi kira kan kasar da ta gaggauta aiwatar da shirin tsuke bakin aljihunta wanda aka amince da shi a watan Janairun da ya gabata

Ta ce zata dau mataki kan kasar idan har hakan bai faru ba.