Yadda yara ke dillancin gwanjo a Maiduguri

Bilkisu
Image caption Wakiliyar BBC Bilkisu Babangida na tattaunawa da yaran dake sana'ar gwanjo a Maiduguri

A kowacce irin al'umma a duniya,yara suna nada bukatar kyakkyawar kulawa ta fuskar kiwon lafiya, zamantakewa da ilimi.

A kasashe masu tasowa kamar Najeriya yanzu haka yara da dama ba sa samun kulawar da ta kamata kamar yadda asusun yara na Majalisar Dinkin Duniya ya jaddadawa kasashen.

Yanzu haka iyaye da dama sun bar daukar dawainiyar yaran wadanda kan fita yin kawadago a kasuwanni domin nema wa kansu abinci da sutura, har ma da kudin makaranta ga wadanda suke karatun.

Babbar matsalar anan ita ce ko wannan dawainiyar kan bari yaran su mayar da hankulan su wajen karatun?

Rayuwar yara akan titina

Wakiliyar mu dake Maiduguri Bilkisu Babangida ta ci karo da wasu kananan yara yan shekaru bakawi, tara da kuma goma sha daya da kan yi dillancin kayan gwanjo bayan sun tashi daga makaranta.

Tace babu shakka wadannna yaran za a iya cewar suna daga cikin wadanda suka yi sa'a fiye da daruruwan yaran da basu samu halin shiga makarantar ba.

To sai dai su din ma kamar ace al'amarin ya zama jakin doki, domin akasarin rayuwar su na kasancewa a bisa tituna da zarar sun ta shi daga makaranta domin sukan tafi yawon dillanci don tafiyar da rayuwar su ta yau da kullum.

Talauci na daga cikin abubuwan da aka bayyana da kan sa iyaye su kyale 'ya'yan nasu cikin wannan hali na daukar dawainiyar kansu.

Image caption Wasu yara masu sana'ar gwanjo a Maiduguri-Najeriya

Hira da yaran

Yawancin yaran da wakiliyar BBC Bilkisu Babangida ta tattauna da su sun bayyana cewa tallan kayan ake ba su.

Sannan idan suka samu kudin sukan kaiwa iyayen su, yayinda a bangare guda sukan raba dawainiya a tsakani su da iyayen.

Daya daga cikin yaran ya ce a rana yakan samu naira dari ko hamsin daga tallan da yake yi, inda a karshe yakan kaiwa iyayensa kudin.

Yaran dai sun ce duk da wannan sana'a da suke yi, suna samun damar zuwa makaranta.

Saurari rahoton Bilkisu

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Illoli

Hajiya Hauwa Usman Aliyu ta Kungiyar Mata Musulmi ta kasa FOMWAN a jihar Borno, ta bayyana irin illolin hakan da cewar yaran ba za su iya samu mayar da hankulan su wajen daukar darasi ba.

Muddum dai suna kasancewa a cikin irin wannan hali na talla da daukar dawainiyar kansu bayan sun ta shi daga makaranta.

Tace yaro tun yana karami idan bai samu tarbiyya mai kyau ba, to ba zai taso cikin rayuwa ingantacciya ba.

Baiwa kananan yaran 'yancin samun wadataccen ilimi, wata babbar fa'ida ce da hukumomi ya kamata su yi tsayuwar daka wajen kulawa domin gujewa karuwar talauci da jahilci da ya addabi kasashe da dama.