Hukumar EFCC za ta binciki Maurice Iwu

Maurice Iwu
Image caption Tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa Maurice Iwu

A Najeriya, hukumar dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati wato EFCC ta ce za ta gudanar da bincike akan zargin aikata ba dai dai ba kan tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa Farfesa Maurice Iwu.

Ana dai zarginsa ne da salwantar da naira miliyan dubu biyu da dari takwas daga asusun hukumar zaben kasar.

Hukumar ta EFCC ta kuma ce za ta gudanar da binciken ne da zummar hukunta duk wanda ya aikata ba dai-dai ba akan batun.

Mai magana da yawun hukumar Femi Babafemi ya shaidawa wakilin BBC Nasidi Adamu Yahaya, cewa hukumar ba za tayi binciken bane domin yai masa bita-da-kulli.

Sai dai kawai domin tabbatar da cewa ana tafiyar da ayyukan gwamnati yadda ya kamata.