Yansandan kasa da kasa sun cafke Ibori a Dubai

Interpol
Image caption An kama Ibori ne dai a Dubai

Hukumar yaki da yiwa tattalin arziki zagon kasa ta Nigeria, watau EFCC ta bayyana cewar yan sanda a Dubai sun kama tsohon gwamnan Jihar Delta, James Ibori.

Hukumar ta ce tuni ta fara kokarin hadin guiwa tsakaninta da hadaddiyar daular larabawa don ganin an taso keyar tsohon gwamnan na Jihar Delta, zuwa Najeriya don fuskantar hukunci.

Hukumar ta EFCC ta ce za ta tabbatar a wannan karon, Cif Ibori ya fuskanci shari'a don nunawa duniya cewar da gaske ta ke yi wajen yaki da cin hanci da rashawa.

James Ibori dai ya yi ta wasan buya da hukumar ta EFCC bayan da ta ayyana shi daya daga cikin jerin mutanen da ta ke nema ruw ajallo a duniya.