Shugaban jam'iyyar PDP yayi murabus

Shugaban jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya, Vincent Ogbulafor, ya sauka daga kan mukaminsa kwanaki hudu bayan ya gurfana a gaban wata kotu saboda tuhumarsa da aka yi da aikata laifuffuka goma sha shida, ciki har da cin hanci da rashawa.

Shi dai Mista Ogbulafor, tare da wadansu mutanen uku, sun musanta zargin cewa sun karbi cin hancin da ya kai na fiye da naira miliyan dari.

Bayan gurfanar da Chief Ogbulafor ne dai rahotanni suka ambato wadansu gwamnoni da ke kudu maso yammacin kasar na shawartarsa a farkon makon nan ya ajiye mukaminsa, matakin da tsohon shugaban na PDP, a lokacin, ya ce ba za ta sabu ba.

To sai dai, a cewar wadansu rahotanni, Mista Ogbilafor ya ci gaba da fuskantar suka daga bangarori daban daban, baya ga matsin lamba daga wadansu ’yan jam’iyyar a kan ya yi murabus.

Wadansu na hanun daman Mista Ogbulafor dai sun yi zargin cewa tsohon shugaban na PDP ya shiga halin tsaka mai wuya ne bayan da ya fito fili a watan Maris ya ce jam’iyyar za ta ci gaba da bin tsarinta na karba-karba, kuma a cewarsa yankin arewacin kasar ne zai fitar da dan takarar jam’iyyar a shekarar 2011.