Har yanzu ana zaman dar-dar a Thailand

Masu zanga-zanga a Gangkok
Image caption Masu zanga-zanga na fuskantar sojoji daga bayan shingaye

Har yanzu hankula na tashe a babban birnin kasar Thailand, wato Bangkok, inda dubban sojoji suka yi kawanya ga sansanin masu zanga-zangar kin jinin gwamnati.

Gwamnatin kasar dai ta gargadi jama'a su gujewa sansanin da masu zanga-zangar, wadanda ake yiwa lakabi da jajayen riguna, suka yi zaman dirshan.

Titunan wannan yankin na birnin Bankok dai, wadanda su kan kasance makil da jama'a a wasu lokutan, kusan fayau suke ba kowa.

Su kuwa masu zanga-zangar suna fuskantar sojojin ne daga bayan wadansu shingaye, wani lokaci ma su takale su.

Da safiyar yau Jumu'a dai rahotanni sun bayyana cewa an yi wata sabuwar arangama.

Rahotannin sun ce masu zanga-zanga sun jejjefa duwatsu da kwalabe a kan sojojin, su kuma sojojin sun yi harbin gargadi a sama.

A daren jiya Alhamis dai yunkurin da masu zanga-zangar kusan su dari suka yi na tunkarar sojojin ya jawo fito-na-fito, al'amarin da ya yi sanadiyyar kashe mutum daya.

Wani jami'in soja wanda ya bijirewa gwamnati kuma na cikin halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai bayan harbinsa da aka yi a daren jiyan.

Gwamnatin ta sha yin barazanar za ta yankewa sansanin masu zanga-zangar wutar lantarki da ruwan sha, ta kuma toshe musu hanyoyin samun abinci.

To amma masu zanga-zangar na da injinan samar da wutar lantarki, wato janareto, da tankunan ruwan sha, da ma wuraren cin abinci.

Ga alamu dai za su dade ba su kawo karshen zaman dirshan din nasu ba.