Ana cigaba da tashin hankali a birnin Bangkok

Zanga zanga a Thailand
Image caption An sami hasarar rayuka a zanga zanga a Thailand

An ji karar fashewar abubuwa da kuma harbe harben bindiga a Bangkok, babban birnin Thailand.

Yayin da rana ta fadi, har yanzu dakaru na ta kokarin sake karbe iko da tsakiyar birnin na Bangkok, inda masu zanga zangar nuna kyamar gwamnati suka yi kaka gida.

Mutane biyu ne suka mutu lokacin artabun, yayin da wasu akalla arba'in da biyar suka ji raunuka, ciki harda 'yan jarida uku, a artabu na baya bayan nan.

Masu zanga zangar sun kone wata motar bas, tare da kai hari a kan wasu ababen hawa, domin katse wa sojoji hanzari. Suna so ne gwamnatin kasar ta yi murabus, domin a gudanar da sabbin zabubuka.