An rabawa kananan yara abinci a Nijar

Rabon kayayyakin abinci
Image caption Gwamnati da Majalisar Dinkin Duniya na samar da abinci cikin sauki

A jamhuriyar Nijar, an rabawa miliyoyin kananan yara 'yan kasa da shekaru biyu da haihuwa kayan abinci mai gina jiki domin ceto su daga fadawa cikin matsanciyar tamowa.

Hakan dai na zuwa ne yayin da ya rage 'yan sa'oi kalilan Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatin mulkin sojan Nijar din su kaddamar da wani gagarumin shirin rarraba abinci a garin Tudun Alhaji a Jihar Tahoua (Tawa) da ke arewacin kasar.

Shirin zai samar da kayayyakin abincin da suka hada da shinkafa da dawa ga mutanen da yawansu ya kai miliyan daya da dubu dari biyar, da nufin baiwa al’ummar kasar damar tunkarar ayyukan damuna cikin kwanciyar hankali.

Kasar ta Nijar dai na fuskantar matsalar karancin abinci a bana, inda akalla mutane miliyan takwas ke bukatar tallafi.