Ana ci gaba da taho-mu-gama a Thailand

Masu zanga-zanga
Image caption Masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a Thailand na sa wuta a kan titunan Bangkok

Ana ci gaba da mummunar taho-mu-gama a babban birnin Thailand, wato Bangkok, tsakanin sojojin gwamnati da kuma sansanin masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin, wadanda aka yiwa lakabi da jajayen riguna.

A arangamar da aka fara tun ranar Alhamis dai, akalla mutane goma sha shida ne suka rasa rayukansu, wadansu dari da hamsin kuma suka yi rauni.

Masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin sun yi ta dauki-ba-dadi da sojoji cikin dare a kewayen sansanin masu zanga-zangar da ke tsakiyar birnin Bangkok.

Wani sabon fadan ya sake barkewa da wayewar garin yau a wurin, inda aka kashe fiye da mutane goma sha biyu jiya Juma'a.

A wurare da dama a tsakiyar Bangkok dai ba shiga ba fita ko da yake harkoki na gudana kamar yadda aka saba nesa da inda masu zanga-zangar suke.

Gwamnati ta ce tana kokarin ganin ta kawo karshen zanga-zangar, ta kuma hana makamai kai-kawo a tsakanin jama'a don takaita asarar rayuka.

A cewar gwamnatin, lokacin tattaunawa da masu zanga-zangar ya wuce.

Sai dai masu zanga-zanagar, wadanda suka samu karin abinci da ruwan sha, kuma kashe-kashen baya-bayan nan suka fusata su, sun ce ba za su watse ba har sai an kira sababbin zabubbuka.