Amurka na neman tabbaci daga kamfanin BP

Tambarin kamfanin mai na BP
Image caption Kamfanin BP ya ce zai bayar da kudin da ake bukata don share man da kuma duk wata diyya da ta kamata

Gwamnatin Amurka ta bukaci tabbaci nan take daga kamfanin mai na BP cewa lallai kamfanin zai biya kudin da ake bukata don magance kwarar danyen man fetur a Mashigin Tekun Mexico.

A wata wasika da suka aikewa kamfanin na BP, Sakataren Harkokin Cikin Gida Ken Salazar da takwararsa ta Harkokin Tsaron Cikin Gida Janet Napolitano, sun ce al'ummar kasar na da hakkin sanin hakikanin manufar kamfanin.

Wasikar da gwamnatin Obaman ta aikewa kamfanin na BP dai na bukatar kamfanin ne ya fayyace yawan kudin da zai biya.

A makon da ya gabata shugaban reshen Amurka na kamfanin ya ce kamfanin zai biya dukkan kudin da ake bukata don share man da ya kwarara da kuma duk wata diyya da ke bisa ka'ida.

Sai dai gwamnatin ta Amurka tana bukatar tabbaci daga kamfanin cewa zai yi hakan.

A halin da ake ciki kuma ana ci gaba da yunkurin tsayar da kwarar man.

Babban jami'in gudanarwa na kamfanin na BP, Doug Suttles, ya bayyanawa manema labarai cewa kamfanin zai sake yunkurin zura wani bututu a rijiyar da ke kwarara don zuke man a daren jiya Asabar.

Mista Suttles ya kara da cewa sinadaran da aka fesa ranar Juma'a a mabubbugar man don su tsinka shi sun fara yin tasiri.

An lura cewa yawan man da ke haurowa saman tekun ya ragu, alamar da ke nuna cewa danyen man yana tsinkewa.