Iran ta cimma 'yarjejeniya da Turkiya

Shugabannin Iran da Turkiya da Brazil sun kulla 'yarjerjeniya
Bayanan hoto,

Shugabannin Iran da Turkiya da Brazil sun kulla 'yarjerjeniya

Iran ta sa hannu a kan wata yarjajeniya tare da kasashen Turkiyya da Brazil, wadda a karkashin ta, Iran din za ta tura karfen uranium din da ta sarrafa zuwa kasashen.

A maimaikon haka, ita kuma za a ba tasharta ta nukiliya da ke Tehran, makamashi.

Wannan matakin zai iya yin babban tasiri a sabuwar tattaunawar da kasashe ke yi, kan batun sawa Iran takunkumin karya tattalin arziki game da shirinta na nukiliya.

Sai dai, Shugaban majalisar kasashen turai, Herman van Rompuy, ya ce matsayin majalisar tarayyar Turai kan saka wa Iran din takunkumi ba boyayye ba ne.