Janar a kasar Thailand ya rasu

General Khattaya Sawasdipol
Image caption An harbe General Khattaya Sawasdipol lokacin zanga-zanga

Wani janar a kasar Thailand wanda ya shiga zanga zangar masu adawa da gwamnati kuma aka harbe shi a ka ranar alhamis da ta gabata ya rasu.

An harbe General Khattaya Sawasdipol, ne jim kadan bayanda aka fara kokarin tarwatsa masu zanga zangar daga cibiyar birnin wanda har yanzu ake kai.

Gwamnati ta ce mutane 35 ne suka rasu kuma kimanin dari biyu da arba'in da hudu sun samu raunuka.

Sun sanya wa'adi ga mutanen da su bar sansanonin kafin tsakiyar yau litinin.