An daidaita tsakanin ma'aikatan Nitel da ministar yada labaran Najeriya

Ministar yada labara da sadarwa  ta Nijeriya
Image caption Ministar yada labara da sadarwa ta Nijeriya

A Najeriya Kungiyar Ma'aikatan kamfanin Sadarwa na NITEL da kuma MTEL ta ce ta gana da ministar ma'aikatar sadarwar kasar Madan Dora Akunyili dangane da zanga zangar da suka gudanar kan hakkokinsu.

Kungiyar ta ce, a ganarwar ta su ministar ta yi masu alkawarin cewa za'a kafa wani kwamiti na musaman wanda zai ziyarci fadar gwamnatin kasar domin ya shigar da kuka a gaban shugaban kasar Dakta Goodluck Jonathan dangane da albashin su da kuma hakkokinsu.

Da ranar Talatar ne ma'aikatan NITEL din suka gudunar da zanga zanga a wajen ofishin ginin ministar sakamkon rashin biyan su albashin sama da shekaru biyu.

Masu zanga-zangar sun rufe kofar shiga ginin ma'aikatar a Abuja babban birnin tarayyar kasar.

A cewar masu zanga zangar, yau fiye da shekaru biyu kenan da gwamnatin Najeriyar ke jan kafa wajen biyan su albashi, lamarin da suka ce ya jefa su cikin wani hali na ha'ula'.

Ministar ma'aikatar Farfesa Dora Akunyili ce ta nemi tattaunawa da shugabannin kungiyar domin neman masalaha.