An kafa sabuwar majalisa a Burtaniya

Pira Minista David Cameron da mataimakinsa Nick Clegg
Image caption Pira Minista David Cameron da mataimakinsa Nick Clegg

Pira ministan Burtaniya David Cameron ya yi maraba da sabbin 'yan majalisar dokokin kasar, yana mai cewa wata alama ce ta dasa sabuwar alkiblar siyasar kasar, yana dai zaune ne kusa da mataimakinsa Nick Clegg.

Sabuwar gwamnatin hadin gwuiwar da aka kafa a makon da ya gabata ce ta baiwa shugabannin jam'iyyun biyu damar zama a teburi guda. Ita ma shugaban jam'iyyar Labour ta riko Harriet Harman, ta taya sabon Pira Ministan murna tana mai cewa jam'iyyarta za ta sa masa ido sosai.

Duk da irin adawar da ya fuskanta, an sake zaben John Bercow a matsayin shugaban majalisar, inda yayi alkawarin tafiya tare da kowa.

Sai ranar Laraba ne za a rantsar da 'yan majalisar, amma sun dawo ne domin su zabi shugaba, wanda a ka'ida ake sake zaba nan take.

Allawadai da shugaban Majalisar

An samu rudani bayanda wasu 'yan majalisa suka nuna rashin amincewa lokacin da aka gabatar da sunan mista Bercow domin asake zabensa, sai dai akawun majalisar ya ce masu goyon bayan shugaban ne suka yi nasara.

Mista Bercow ya zama shugaban majalisar ne bara lokacin da aka matsantawa Michael Martin yin murabus sakamakon badakalar kudaden alawus na 'yan majalisar, mafi aka sari da goyon 'yan jam'iyyar Labour.

Duk da cewa shi dan jam'iyyar Conservative ne tun kafin ya zamo shugaba, wasu daga cikin 'yan majalisar sun zarge shi da laifin nuna banbanci.

Sai dai ya samu goyon bayan manyan 'ya'yan jam'iyyar Conservative, irinsu Sir Malcolm Rifkind, wanda ya shaidawa 'yan majalisar cewa duk da bai zabe shi ba bara, amma ya yaba da rawar da ya taka a watanni 11 da suka gabata.

Amma yayinda 'yan adawa suka kasa samun kuri'a, sai magoya bayansa suka zaunar da shi akan kujerar shugabanci kamar yadda tarihin majalisar ya gada.

An rushe da dariya lokacin da mista Bercow ya nemi Pira Minista da yayi magana, sannan aka samu dan tsaiko-lokacin da wasu 'yan majlisar suka dinga yiwa Mista Cameron taken kaine..kaine...

An cika majalisar

Sabon Pira ministan ya bayyana farin cikinsa da sake zabar Mista Bercow duk da irin matsanancin kalubalen da ya fuskanta.

Majalisar Commons din dai ta cika sosai a zaman ta na farko tun bayan zabeinda yasa wasu 'yan majalisar ma ba su samu wurin zama ba.

A jawabin da ya gabatar, mista Cameron ya ce an samu sabbin 'yan majalisa ciki harda mata da bakaken fata da kuma 'yan nahiyar Asiya.

Mista Cameron ya kara da cewa "wannan wata alamace ta sabuwar alkiblar siyasar Burtaniya, kuma dama ce ga sabbin 'yan majalisar na su fahimci yadda al'amura ke tafiya anan."

Ya kara da cewa babban dadin shi ne na gina amintaka tsakanin 'yan majalisa da kuma jama'a, tare da aiwatar da abin da ya dace.

Wannan na nufin yan zu Mista Harman tare da sauran 'ya'yan jam'iyyar Labour za su zauna a matsayin 'yan adawa a karon farko tun shekarar 1997.

Cikakkiyar adawa

Ta shawarci sababbin 'yan majlisar da su maida hankali wajen koyar al'amura cikin shekaru goma masu zuwa.

Ta gayawa Pira Minista cewa, " ina taya ka murna, kuma lallai akwai jan aiki a gaban ka".

"Duka mun amince da bukatar samun cikakkiyar gwamnati, amma har ila yau akwai bukatar samun adawa mai karfi".

Sai dai wani dan jam'iyyar Labour Jim Sheridan, ya soki bukatar da gwamnati ta gabatar ta baiwa 'yan majlisar damar rusa majalisa idan aka samu amincewar kashi 55 cikin dari.

Kimanin sabbin 'yan majalisa 227 ne aka zaba a ranar 6 ga watan Mayu, abinda yasa aka kasa samun jam'iyyar da ke da rinjaye, wanda kuma ya haifar da gwamnatin gamin gambiza tsakanin Conservative da Lib Dems.

A ranar Alhamis mai zuwa ne za a rantsar da sabbin 'yan majalisar inda za a fara da tsofaffi, kafin azo kan sabbi.

Ayyukan majlisar za su kankama ne a mako mai zuwa, tare da jawabin sarauniya-sannan a gabatar da manufofin sabuwar gwamnati a ranar Talata.