Mata na neman kawo sauyi a fagen siyasar Kano

Mata masu zanga zanga
Image caption Zanga zangar mata na kara zamo ruwan dare a Najeriya

A jahar Kano da ke arewacin Nigeria wasu mata sun gudanar da wata zanga zangar lumana zuwa gidan gwamnatin jahar, inda suke kira da a tabbatar da bin tsarin demokradiyya wajen tsayar da yan takara a cikin jam'iyyu.

Matan sun ta yin kabbara tare da ikirarin kawo sauyi a fagen siyasar Jahar.

Wannan mataki da matan suka dauka yazo ne a daidai lokacin da wasu jama'ar jahar ke cecekuce kan yadda gwamnan jahar Malam Ibrahim Shekarau ya nuna goyon bayansa a fili ga wani dan takara daga cikin da dama dake son su gaje shi.

Haka kuma matan sun bayyanawa wakilin BBC Yusuf Ibrahim Yakasai, shirin da suke dashi na shiga a dama dasu a zabuka masu zuwa, inda suke fatan samun cikakken wakilci.

Matan dai sun gudanar da zanga zangar ne cikin lumana a fadar gwamnatin kano, inda suka yi Allah wadai da tsarin zabar 'yan takarar da wasu masu fada a ji cikin jam'iyyu ke yi ba tare da a na gudanar zabukan fidda gwani ba.

Wannan mataki dai da matan suka dauka ba zai rasa nasaba da yadda gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana goyon bayasa a zihiri, ga wani dan takara dake son tsayawa takarar gwaman a jam'iyyar ANPP a zaben 2011.

Image caption Matan sun nemi a basu damar taka rawa sosai a fagen siyasa

Burin su

Hajiya Ladi Ahmad Mijin Yawa, itace ta jagoranci matan, kuma ta shaidawa wakilin mu cewa burin su shi ne na ganin ana yin adalci wajen fidda 'yan takara.

Sannan tace suna son gwamnan ya bar al'umar Kano su zabi wanda suke so, ba tare da karfa-karfa ba.

Ko da dai matan sun so yin tozali da gwamnan jahar su isar masa da sakon su, ba su samu ganinsa ba, sai dai babban sakataren gidan gwamnatin Alhaji Muhammad Garba ya tarbesu.

"Ya kuma shaida musu cewa da ba don mata bane su, to da yayi amfani da karfin mulki wajen korar su".

Amma ya nemi matan da su koma su tattauna da shugabannin su, inda ya yi musu alkawarin ganawa da gwamnan jihar.

Baya ga bukatar tabbatar da adalci wajen fidda 'yan takara, matan kuma na bukatar samun kujeru a matakan gwamnatoci, inda suke son samun damar wakiltar kansu dan kare muradunsu.

Wasu daga cikin matan sun bayyana aniyar su ta tsayawa takara, da kuma ba su mukamai masu tsoka a gwamnati.

Masu sharhi kan al'amuran siyasa dai na kallon irin wadannan matakai da mata ke dauka a matsayin wasu hanyoyi na nunawa hukumomi irin tasirin da suke dashi a bangaren siyasar Najeriya.

Musamman a fafutukar da suke ta samun kujeru a majalisun dokoki da kuma na zartarwa a duka fadin kasar musamman a zabukan 2011, da yanzu haka ke kara karatowa.