An rantsar da Namadi Sambo mataimakin shugaban kasa

Namadi Sambo
Image caption Sabon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Muhammad Namadi sambo

A Najeriya an rantsar da sabon mataimakin shugaban kasar Alhaji Namadi Sambo.

Babban alkalin kasar mai shari'a Katsina-Alu ne ya jagorancin rantsuwar, a wani biki da aka gudanar a fadar gwamantin kasar da ke Abuja.

Bikin ya samu halattar shugaban kasa Dakta Goodluck Jonathan da gwamnoni da ministoci da sauran jami'an gwamnati.

Har ila yau bikin ya samu halattar shugaban majalisar Wakilai Dimeji Bankole da wasu daga cikin 'yan majalisar kasa.

A farkon makonan ne shugaba Goodluck Jonathan ya mika sunan Namadi Sambo, wanda shi ne gwamnan Kaduna kafin yanzu, a matsayin sabon mataimakin sa.

A gobe Alhamis ne ake saran za a rantsar da mataimakin sa mista Patrick Ibrahim Yakowa a matsayin sabon gwamnan jihar Kaduna, wanda shi kuma daga baya zai zabi na sa mataimakin.

A karshe shugaban kasa ya bashi lambar yabo da girmamawa ta GCON, kamar yadda tsarin mulki ya ta nada.

Damuwa

Jama'a sun nuna damuwa a mahaifarsa ta jihar Kaduna, game wanda zai maye gurbinsa idan ya tafi.

Kaduna dai itace cibiyar mulki ta arewacin Najeriya, kuma abaya an sha fama da rikicin addini da na kabilanci a jihar.

Sai dai shugabannin addini da siyasa s

un yi kiran da a kwantar da hankali, suna masu cewa zaben gwamna Namadi zai haifar da ci gaba ga jihar.

Shi ma gwamna Namadi ya bayyana kwarin gwiwa ga mataimakin na sa yana mai cewa mutumne da babu shakka zai iya daukar kalubalen da ke gabansa.

Cancanta

Wasu da dama na ganin Namadi Sambo a matsayin wanda bai cancanci mukamin ba.

Editan BBC na Abuja Ahmed Idris, ya ce Namadi Sambo ba fitacce bane a siyasance, kasancewar ba a sanshi ba kafin ya zamo gwamna, kuma sunansa ba ya cikin wadanda aka saran za a zaba tun farko.

Har ila yau ana ganin shugaban ya zabe shi ne domin ba shi da go

gewar da zai iya kawo masa kalubale a siyasance.

Yayinda wasu ke ganin wani sabon salo ne na tafiyar da al'amura da shugaban ke son fitowa da shi.

Zaben shekara ta 2011

Masana siyasa na ganin duk wanda aka nada shi ne zai zamo dan takarar jam'iyyar PDP mai mulki a zabe mai zuwa.

Har yanzu dai bau tabbas ko shugaba Jonathan zai tsaya takara a zaben ko kuma a'a.

Amma an rawaito daya daga cikin masu yi masa hidima, yana cewa shugaban zai tsaya takarar, amma daga bisani ya janye zancen nasa, yana mai cewa ba haka yake nufi ba.

Ita dai jam'iyyar PDP ta ce dan takarar ta zai fito ne daga Arewacin kasar, saboda yarjejeniyar da ta cimma ta raba iko tsakanin yankunan kasar.

Amma ana hasashen Jonathan zai yi kokarin kaucewa wannan yarjejeniya domin ci gaba da mulki.

Rade radi

A baya dai anta rade-radin cewa za a bada mukamin ne ga mutane daban daban, wadanda suka hada da sakataren gwamnatin tarayya Yayale Ahmed.

Haka kuma sunan tsohon gwamnan jihar Kaduna Sanata Ahmed Makarfi ma ya fito a sahun wadanda ake saran baiwa mukamin.

Baya ga gwamnan jihar Jigawa wanda aka dade ana magana akan yiwuwar ba shi, tare da takwaransa na jihar Niger Babangida Aliyu, akwai kuma tsohon shugaban hukumar EFCC Malam Nuhu Ribadu.

Har ila yau akwai rahotannin da suka nuna za a iya mika sunan gwamnan jihar Katsina Shehu Shema dana Kebbi Sa'idu Dakin Gari dana Bauchi Isa Yuguda da mataimakin gwamnan jihar Sokoto Muntari Shagari.

Kama kafa

Jama'a da kungiyoyi da dama sun ta kokarin kama kafa domin ganin an nada wanda suke so.

Su kansu kungiyar Sanatocin Arewacin kasar sai dai suka bada sanarwar marawa Sanata Makarfi baya.

Yayinda rahotanni suka nuna cewa kungiyar gwamnonin kasar ta yi kokarin ganin an nada daya daga cikinsu.

Ko me ake ciki dai, alammu na nuna cewa siyasar kasar na shirin fuskantar gagarumin sauyi, domin kawo yanzu duk hasashen da aka yi abaya ya rushe, tun bayan rasuwar marigayi shugaba Umaru Musa 'Yar'adua.