Taimakon abinci kashi 45 ne ya zo hannu a Niger

Yuwa a Niger
Image caption Gwamnati mulkin Sojin, Nijar ta ce kasar na fama da matsalar yunwa

A jamhuriyar Niger an kammalla wata ganawa tsakanin fira ministan kasar Dokta Mahammadu Danda da tawagar wakillan kasashe da kungiyoyi masu hannu da shuni da suka hada da tarayyar Turai da Amurka da makamantansu.

Wannan ganawa dai ta yi bitar ayyukan bada agaji ga jama'ar Niger bayan da hukumomin mulkin sojan Niger din suka yi shelar cewa akwai yunwa a Niger din.

Sannan suka ce kimanin mutane miliyan takwas ne ke bukatar agajin abinci.

Fira Minista Dakta Muhammad Danda, ya shaidawa wakilin BBC Iddy Bara'ou cewa, daga cikin bukatocin Niger din na kayan abinci, kashi 45 daga cikin dari ne kawai ya samu, watanni biyu bayan shelar.

Tun bayan da ta kwace mulki a watan Fabrerun da ya gabata, gwamnatin mulkin sojin Niger ta bayyana cewa kasar na bukatar daukin abinci sakamakon matsalar yunwar da ake fama da ita.

Abinda gwamnatin da ta gada ta Malam Tanja Mamadou ya sha musantawa abaya.