An yankewa 'yan luwadi shekara 14 a gidan yari

'yan Luwadi a Malawi
Image caption 'Yan luwadin da suka yi aure a Malawi, amma kotu taki amincewa

Wani alkali a Malawi ya yankewa wasu matasa biyu hukunci daurin shekaru 14 a gidan yari tare da gwale-gwale, bayan da ya same su da laifin ayyukan batsa da kazanta.

Steven Monjeza, 26, da Tiwonge Chimbalanga, 20, sun kasance a gidan yari tun bayan da aka kamasu a watan Disamban bara, bayan da suka amince suyi aure.

Kaman na su ya fuskanci adawa daga kasashen duniya da kuma cece-kuce kan makomar luwadi a kasar.

"Gani ga wane"

"Zan yanke muku hukunci mai tsauri domin kare sauran jam'ar gari daga mammunan halin ku, sannan ya zamo darasi ga jama'a,"inji mai shari'a Nyakwawa Usiwa-Usiwa.

Lauyan da ke kare mutanen Mauya Msuku, ya ce hukuncin yayi tsauri ganin cewa abinda mutanen suka aikata bai yiwa kowa illa ba.

Amma a cewar Michelle Kagari, mataimakiyar Darakta ta kungiyar Amnesty International a Afrika, "an wuce gona da iri".

Ta bayyana mutanen da cewa basu taka hakkin kowa ba, sannan tace kungiyar za ta ci gaba da kokarin nemo musu hakkinsu. Malawi kasa ce ta masu tsatstsauran ra'ayi inda ake allawadai da auren jinsi daya.

Kuma alkalin ya bayyana auren jinsi daya da cewa ya sabawa al'adar Malawi.

Tsarin doka

Sai dai Peter Tatchell, dan fafutukar kare auren jinsi guda a Burtaniya, yace an kirkiri dokar ne alokacin mulkin mallaka.

"Wannan dokar ta kasashen waje ce, ba Afriaka ba" inji shi.

Mutanen dai sun musunta zargin kuma lauyan su yace an sabawa hakkin da tsarin mulki ya basu.

Wakilin BBC Raphael Tenthani, da ke Blantyre, babban birnin Malawi, yace gwamantin kasar na fuskantar matsin lamba daga kasashen yamma wadanda ke bada agaji.

Kuma ga kasar da ke fama da talauci, inda kashi 40 cikin dari na kasafin kudinta ya dogara kan tallafi daga kasashen waje, wajibi a dauki wannan damuwar da mahimmanci.