Ana hana jaridun Sudan su buga labaru

Shugaba al Bashir na Sudan
Image caption Wadansu jaridun Sudan biyu sun zargi hukumar tsaro da hanasu buga labaru

Wasu jaridun kasar Sudan biyu sun ce kasar na kokarin komawa bisa mulkin kama-karya bayan gwamnati ta tace labarun da suka buga.

Gabanin zabukan watan jiya ne dai hukumomin kasar suka dakatar ta tace bayanan da kafofin yada labarai ke wallafawa a wani mataki na fadada 'yancin fadin albarkacin baki.

Editan jaridar Ajras al Hurriya ya shaidawa BBC cewa wasu jami'an hukumar tsaro ta kasar Sudan din uku ne suka je ofishin jaridar ranar Laraba, 8 ga watan Mayu, inda suka haramta wallafa labaru da dama ta yadda ba zai yiwu jaridar ta fita washegari Alhamis ba.

Shi ma editan jaridar Al Sahafa ya ce hukumar tsaron kasar ta haramtawa jaridar tasa wallafa biyar daga cikin labarun da ta yi niyyar wallafawa.

Editocin biyu sun ce labarun da aka haramta wallafawar sun kunshi bayanai ne a kan yankin Darfur da kuma halin siyasar kasar a yanzu.

Sai dai hukumar tsaron kasar ta ki ta ce uffan a kan batun.

A watan Satumban da ya gabata ne dai gwamnati ta soke dokar da ta baiwa hukumar tsaron kasar ikon tace bayanan da kafofin yada labarai suke wallafawa.

Yarjejeniyar da kudanci da arewacin kasar suka sanyawa hannu a shekarar 2005, wadda ta kawo karshen yakin basasar da suka shafe shekaru suna gwabzawa, ta bukaci a yi zabe cikin wani yanayi da kowa ke da 'yancin fadin albarkacin bakinsa.

Sai dai wannan mataki da hukumomin ke dauka ya sanya ’yancin fadin albarkacin bakin na fuskantar barazana.