Yakowa ya zama gwamnan Kaduna

Patrick Yakowa
Image caption Sabon gwamnan Jihar Kaduna, Mista Patrick Yakowa

An rantsar da Mista Patrick Yakowa a matsayin gwamnan jihar Kaduna, bayan Shugaba Goodluck Jonathan ya nada tsohon gwamnan jihar Namadi Sambo Mataimakin Shugaban kasa.

An yi ranstuwar ne a wani kasaitaccen biki da aka gudanar a jihar ta Kaduna.

Wakilin BBC Nura Mohammed Rigim wanda ya halarci bikin, ya ce 'yan siyasa da jama'ar gari musamman daga kudancin jihar sun cika makil a wurin bukin.

Ya ce manya baki da suka halarci bikin rantsarwar sun hada da tsohon gwamnan Kaduna, Sanata Ahmed Mohammed Makarfi.

Ana dai sa ran gwamnan zai fito da suna wanda yake so ya zama mataimakin sa cikin 'yan kwanaki kadan.

Patrick Ibrahim Yakowa

Mista Patrick Yakowa dai shi ne matakin gwamna kafin a nada shi gwamnan jihar.

Gwamna Patrick Yakowa dai ya fara zama mataimakin gwamna ne bayan rasuwar tsohon mataimakin gwamna Mista Stephen Shekari a shekarar 2005..

Bayan an kammala wa'adin mulkin ne Mista Yakowa ya tsaya takara da Alhaji Namadi Sambo a matsayin mataimakin sa karkashin Inuwar Jam'iyyar PDP a Shekarar dubu da bakwai.

Gwamna Patrick Yakowa dai ya yi Ministan ma'adanai a gwamnatin sojin Janar Abdussalami Abubakar, sannan kuma ya zama Sakataren gwamnatin jihar Kaduna a shekarar 2003, kafin ya hau kujerar mataimakin gwamna a shekarar dubu biyu da biyar.