Arsenal ta dauki Marouane Chamakh

Arsenal ta dauki Chamakh
Image caption Arsenal ta dade tana neman Chamakh

Arsenal ta dauki dan wasan kasar Morocco Marouane Chamakh, wanda ta dade tana nema ruwa a jallo.

Dan wasa mai shekaru 26, wanda aka dade ana danganta shi da Arsenal tun kakar wasa ta bara, zai je ne a kyauta.

A watan Febreru, ya bayyana cewa Liverpool da Tottenham da Arsenal, duk sun yi zawarcin sa.

"Ba tare da kokonto ba, Arsenal ne klub din da na fi so," inji dan wasan, wanda ya zira kwallaye 79 a shekaru takwas din da shafe a Bordeaux.

Ya kara da cewa burin sa shi ne na yazo Arsenal, saboda ya dade yana goyan bayan su.

"Akwai kwararrun 'yan wasa a Arsenal, kuma zan yi iya kokarina wajen taimakawa klub din domin ganin ya dauki kofi a kakar wasa mai zuwa".