Gwamnatin Najeriya za ta binciki Janar Babangida

Taswirar Najeriya
Image caption An dade ana zargin shugabannin Najeriya da aikata badai dai ba

A Najeriya gwamnatin tarayyar kasar ta ce za ta kafa wani kwamatin da zai binciki tsohon shugaban mulkin sojan kasar Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

Gwamnatin za ta binciki tsohon shugaban ne kan zargin da wata kungiya ta yi cewa ya warure kudi fiye da dala biliyan goma sha biyu a lokacin da ya ke kan karagar mulki.

Gwamnatin ta ce za ta kuma gurfanar da Janar Babangidan a gaban kuliya don yi masa shari'a idan sakamakon binciken ya nuna cewar lallai ya warure wadannan kudade.

Ministan shari'a na kasar Muhammad Adoke ya ce wajibi ne gwamnati na bincika al'amarin domin daukar matakin da ya dace. Sai dai a nasa bangaren Janar Babangidan ya ce gwamnatin za ta yi binciken ne don yin zagon-kasa a aniyarsa ta yin takarar shugabancin kasar a shekarar mai zuwa.