Tarayyar Turai za ta shawo kan matsalar tattalin arzikinta

Matsalar kudi a Turai
Image caption Yadda darajar Yuro ta kasance tsakaninta da dala a watanni 3 da suka wuce

Shugaban hukumar gudanarwa ta tarayyar turai, Herman Van Rompuy, ya ce ya yi imanin cewa tarayyar turan zata iya shawo kan matsalar tattalin arzikin da ake fuskanta a sakamakon dimbin bashi, da kuma faduwar darajar takardar kudin euro.

Ya bayyana haka ne a Brusels, bayan taron ministocin kudi don neman matakan yin kandagarki.

Ya ce ana bukatar koyon darasi daga wannan mawuyacin hali. A baya an rika daukar matakai a makare.

tun da farko ministocin kudin Kungiyar Tarayyar Turai sun yi taro a birnin Brussels inda suka tattauna matsalar da ake fuskanta a kasashen da ke amfani da kudin Euro.

Babban abinda za suka maida hankali akai shi ne shawarar da hukumar Tarayyar Turai ta bayar na karin sa ido da ma wani tsoma baki a cikin kasafin kudin kasashe wakilan kungiyar.

A karshen taron, ministocin, sun amince a rika daukar matakan rage gibin tattalin arziki.

Majalisar dokokin Jamus ta amince da gudunmawar dala trillion guda, da kasar zata ba da a asusun tallafa wa kasashen da ke amfani da takardar kudin bai daya ta euro.

An dai tafka muhawara, kafin a amince da bukatar.

Jamus din ce za ta bada kashi daya cikin biyar na kudaden, wadanda tarayyar turai ta amince da su makonni biyun da suka wuce.

Kasashen turai dai sun dade suna fama da matsalar sakamon rikicin bashin da Girka ta samu kanta a ciki.

Abinda kuma ke barazana ga sauran kasashen da ke amfani da takardar kudi ta Yuro.

Takardar kudin ta Yuro dai na ci gaba da faduwa a kasuwannin musayar kudade ta duniya, abinda yasa kasahen ke tashi-fadin ganin sun shawo kan matsalar.