Ministocin kudi na Turai na yin Taro a Brussels

Matsalar kudi a Turai
Image caption Yadda darajar Yuro ta kasance tsakaninta da dala awatanni 3 da suka wuce

Ministocin kudi Kungiyar Tarayyar Turai na yin taro a birnin Brussels domin tattauna matsalar da ake fuskanta a kasashen da ke amfani da kudin Euro.

Babban abinda za a maida hankali akai shi ne shawarar da hukumar Tarayyar Turai ta bayar na karin sa ido da ma wani tsoma baki a cikin kasafin kudin kasashe wakilan kungiyar.

Taron na zuwa ne adai dai lokacin da majalisar dokokin Jamus ta amince da adadin kudin da kasar za ta ware domin ceto tattalin arzikin kasashen da ke amfani da takardar kudin. Wakilin BBC kan harkokin tattalin arziki Andrew Walker ya ce wannan na yin kamanni da irin yadda Amurka ke tafiyar da kudadenta na Gwamnati.

Kasashen turai da sun dade suna fama da matsalar sakamon rikicin bashin da Girka ta samu kanta a ciki.

Abinda kuma ke barazana ga sauran kasashen da ke amfani da takardar kudi ta Yuro.

Takardar kudin ta Yuro dai na ci gaba da faduwa a kasuwannin musayar kudade ta duniya, abinda yasa kasahen ke tashi-fadin ganin sun shawo kan matsalar.