Ra'ayi Riga: Me ke janyo yawan gobara a kasuwanninmu

Gobarar kantin kwari
Image caption Gobarar kantin kwari

Matsalar gobara a kasuwanni dai matsala ce da ake fama da ita a kasashenmu. Ko da a baya bayan nan, wuta ta tashi a kasuwar Agugo-loshi da ke yammacin birnin Accra na Ghana.

Haka kuma an yi gobarar a kasuwar 'Marche Congo' da ke birnin Douala na Kamaru. Kasuwanni da dama a Nigeria, a birane irinsu Kano da Bauchi da Katsina da Maiduguri da kuma Anatcha ma wutar ta shafe su.

An yi asarar dimbin dukiya, sannan a wasu lokutan har ma da asarar rayuka da kuma samun raunuka.

Wasu alkalumma daga ma'aikatar cinikayya ta jahar Kano a Najeriya sun nuna cewa, daga bara ya zuwa yau, an samu tashin gobara a kasuwannin 3 na birnin, watau kasuwar Yan Katako a bara da Kantin Kwari a watan Maris da ya gabata, da kuma Kasuwar Kurmi, inda gobarar ta tashi har sau biyu, a bara da kuma watan jiya.

Kodayake Hukuma ta ce ba a samu asarar rayuka ba, amma kiyasin jimlar asarar dukiyar da aka yi a kasuwannin uku ta zarta Naira biliyan daya da rabi.

To a shirinmu na Ra'ayi Riga na wannan mako mun tattuan ne game da wannan bala'i da kan shafi kasuwanninmu.

Mun kuma gayyato mutanen da abun ya shafa game da matsalar wadanda suka hada da Alhaji Abdullahi Ka-buga na Gidan Labaran a kasuwar Kwantin Kwari da ke kano, wanda ya yi asara mai yawa, sakamakon gobarar da ta tashi a watan Maris a kasuwar.

Haka kuma a Kanon mun gayyaci Alhaji Umar Muhammad Soron Dinki, Darektan ma'aikatar kashe gobara ta jahar. Akwai kuma Alhaji Garba Baba Timoli, shugaban kungiyar 'yan kasuwar Kantin Kwarin. Daga Sokoto kuma mun gayyaci Alhaji Isa Sahabi BanKanu, Shugaban babbar kasuwar Sokoton, kuma mashawarci na musamman na gwamnatin jihar kan harkokin da suka shafi Babbar kasuwar ta Sokoto. Akwai kuma masu saurare da suka bayar da tasu gudummawar a cikin shirin.