An kaddamar da kwamitin bincike a Nijar

Shugaaban gwamnatin mulkin sojan Nijar, Janar Salou Djibo
Image caption Shugaaban gwamnatin mulkin sojan Nijar, Janar Salou Djibo, ya rantsar da 'yan kwamitin binciken masu yin sama da kudin gwamnati, to amma...

Shugaban gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar, Janar Salou Djibo, ya rantsar da mambobin kwamitin da gwamnatin ta kafa domin bincike da hukunta wadanda aka samu da laifin yin sama-da-fadi da dukiyar kasa.

Sai dai a lokacin da ake rantsar da mamabobin kwamitin su talatin da bakwai, wadansu 'yan kasar sun yi korafin cewa daga cikin mambobin kwamitin akwai wadanda ba su cancanta a basu wannan aiki ba, saboda an taba samunsu da laifin cin kudin gwamnati.

Daya daga cikin masu shakku a kan wadansu mambobin kwamitin, Abdoul Aziz Alhadji Ladan na kungiyar MOSADEM mai kare hakkin dan-Adam, ya shaidawa wakilin BBC a Yamai cewa ba ya zaton kwamitin zai yi tasiri.

“Akwai daga cikin [mambobin kwamitin] wadanda suka ci kudin kasa, har suka je suka yi kaso wajen shekara uku da wata hudu…in dai wadannan [mutane] masu dauda ne za su yi [wannan binciken, to] ba za a yi aikin da ya kamata a yi ba”.

Sai dai kakakin gwamnatin, Kanar Goukoye Abdoulkarim, ya ce majalisar mulkin soja ta CSRD ba ta da shakka ko kadan a kan tasirin da kwamitin zai yi.

“Mu daga wajenmu ba shakka ko daya; mun ce za mu girka [hukumar bincike], mun girka ta, kuma ba mu dame mata hannuwa ba….

“[Dangane da] zancen wanda ya yi zaman kaso [kuwa], idan mutum ya yi zaman kaso, in dai ya kare [wa’adin da hukunci ya tanada] ya komo [dan kasa na gari] me ke nan; ba a kara ba shi aiki ne?”

Tun lokacin da suka kwace mulki ne dai shugabannin gwamnatin mulkin sojan Nijar din suka yi alkawarin tsaftace harkokin siyasa da tattalin arziki kafin su mayar da kasar bisa turbar dimokuradiyya.