ECOWAS ta yabawa gwamnatin mulkin sojan Niger

Taswirar Niger
Image caption Taswirar Niger

Wakilin musamman na kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, watau ECOWAS ko CEDEAO, ya bayyana gamsuwarsa kan yadda ake shirye-shiryen mayar da kasar Niger bisa tafarkin demokradiyya.

Janar Abdussalam Abubakar, wanda ya kammala wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Niger din, ya yaba da yadda gwamnatin mulki sojan kasar ke tafiyar da al'amurra tun bayan da ta kawar da gwamnatin Mamadou Tanja a watan Fabrairu. Ya ce yana da kyakyawan fatan sojojin za su mika mulki a lokacin da aka tsayar.

Wakilin na ECOWAS ya kuma ce kungiyar na da niyyar tallafawa Niger, a kokarin da take yi na shawo kan matsalar yunwar da miliyoyin jama'a ke fuskanta a kasar, da kuma game da shirye-shiryen zabubukan da za a gudanar a kasar.