Gimbiya Sarah Ferguson tayi abun kunya akan kudi

Gimbiya Sarah Ferguson
Image caption Gimbiya Sarah Ferguson da tayi abun kunya game da kudi

An dauki hoton vidiyon Gimbiyar York, Sarah Ferguson, yayin da take neman yiwa wani hanyar ganin tsohon mijinta, Yarima Andrew, wanda shine da na biyu, na Sarauniya Elizabeth, kuma wakilin musamman na Birtaniya game da harkokin cinikayya.

Jaridar 'News of the World' ta ce, Sarah Ferguson ta bukaci fiye da dala dubu 700 na Amirka daga wani ma'aikacin jaridar da yayi shigar burtu, kamar dai wani hamshakin dan kasuwa, domin ya sami iso ga Yarima Andrew.

Jaridar ta ce daga baya Gimbiya Sarah Ferguson ta yarda ta karbi dala dubu 40, tana mai cewar, Yariman zai taimaka wajen kulla wata yarjajeniyar cinikayya mai tsoka.

A cewar 'News of the World', ko kadan Yarima Andrew ba shi da masaniya game da lamarin karbar toshiyar.