An mika rahoto kan rikicin boko haram a jihar Borno

Titi a Maiduguri, bayan rikicin Boko Haram
Image caption Rikicin Boko Haram ya janyo asarar rayuka da dukiyoyi masu yawa a birnin Maiduguri.

A Nijeriya, yau ne kwamitin da gwamnatin jihar Borno ta nada domin gudanar da bincike game da rikicin Boko Haram ya gabatar da rahotonsa na karshe.

Kwamitin ya bada shawara kan matakan da suka kamata a dauka domin guje wa sake aukuwar irin wadannan rikice-rikice da kuma yadda ya kamata gwamnatin ta tallafawa wadanda rikicin ya shafa.

Kimanin mutane tamanin da biyar ne wadanda suka yi asarar gidajensu , da dukiyoyi, aka bayyana cewa sun bayyana a gaban kwamitin, domin neman tallafi daga gwamnatin jihar.

Kwamitin dai ya shawarci gwamnatin da ta ba su tallafin da ya kama daga kashi talatin zuwa hamsin cikin dari na irin asarar da suka yi.

Gwamantin jihar Bornon dai ba ta ce za ta maido da asarar da mutane suka yi ba, amma ta yi alkawarin za ta bayar da tallafin da ya dace bayan ta gana da Majalisar gudanarwar jihar.