Amurka da China sun fara tattaunawa kan tattalin arziki da siyasa

Jami'an Amurka da China
Image caption Shugaba Hu Jintao na China da Hillary Clinton

An fara aiwatar da wata tattaunawa ta musaman na kwanaki biyu tsakanin manyan jamian Amurka da kuma China a birNin Beijing. Tattunawar zata yi kokarin ganin cewa ta kara karfafa huldar dake tsakanin kasasahen biyu nan da wasu shekaru masu zuwa.

Wakilin BBC ya ce yanzu haka dai ministoccin amurka kokuma shugabannin ma'aikatun kasar guda goma sha biyar ne ke birnin beijing karkashin jagorancin sakatariyar harkokin wajen amurkan madam hilary clinton da kuma sakataren kudi mista Timothy geitner.

A dayan bangaren kuma ita ma chinar tana da yawan manyan jami'ai kussan haka, wadanda suka halarci taron.

Tattaunawar dai zata maida hankakali kan batutuwan da suka shafi tattalin arziki na wani tsawon lokaci, da kuma mara ma juna akan harkokin siyasa.

Sai dai bisa ga alamu akwai wasu batutuwan da suka kunno kai, da ake ganin cewa jami'an kasasahen biyu zasu maida hankali akai.

Daya daga cikin su shine batun Korea ta Arewa da kuma yadda za'a dauki mataki kan kasar sakamakon nutsar da jirgin ruwan yakin kasar Korea ta Kudu .

Sai dai a lokacin da aka bude taron madam Hilary clinton tayi kira kan china akan tayi aiki tare da ita dangane wannan batu.

A batun da ya shafi tattalin azrkin kuma akwai wasu wurare da kassahen biyu ke cece kuce akai da ake ganin cewa zasu tattauna akai. Amurkan dai da jimawa na korafi kan gibin kasuwanci dake tsakaninta da china.

A yayinda ita kuma chinar na son Amurkan ta dage, matakin ikon kan kayyakin da ake shigowa da dasu daga kassahen waje data kafa kan kasar china. Sai dai jama'a kalilan ne ke ganin cewa zasu cimma masalah a tattaunawar tasu.