Shirin tabbatar da zaman lafiya a jahar Plateau

Asarar rayuka a rikicin Jos
Image caption Asarar rayuka a rikicin Jos

Hukumomi a jahar Plateau sun ce za su kafa hukumar binciko gaskiya da sasanta al'umma, a kokarin da suke na kawo karshen rikice-rikicen da suka dabaibaye yankin.

An bayyana hakan ne a karshen wani babban taron da aka gudanar yau a Jos, babban birnin jahar, wanda ya sami halarcin manya manyan masu fada aji da suka hada da tsoffin gwamnonin jahar, da manyan sarakunan jahar.

Sauran matakan shawo kan tashe-tashen hankulan sun hada da samar wa matasa ayyukan yi, da ware wuraren kiwo domin makiyaya.

Jahar ta Plateau ta yi fama da tashe tashe- hankula dake da nasaba da addini da kuma kabilanci tun farkon wannan shekarar, wadanda suka janyo asarar dimbin rayuka da dukiya.