Barace-barace a Afghanistan

Barace-barace a Afghanistan
Image caption Yadda yara ke sagaraftun neman kalaci a kan titunan birnin Kabul

Wani bincike da BBC ta gudanar ya nuna cewa ana samun karuwar kananan yara da ke barace-barace a kan tituna a kasar Afghanistan.

Nargis, yar shekara 10 da haihuwa, tana fara bara ne da misalin karfe 6 na safe, inda take yawon neman Biredin da za su karya kumallo.

Gidan su na kan wani dutse ne inda suke zaune da iyayanta a daki guda.

Wakiliyar BBC ta ci karo da ita a lokacin da ta shiga wani gida bara, sai dai jama'ar gidan sun ce ba su da biredin da za su bata.

Mahaifinta kuma ba zai iya aiki ba. Ya tasiran tu da shaye-shaye, don haka ba makawa sai ita.

Yadda ake neman mafita

Nargis na daya daga cikin dubban yaran da ke yawo a kan titunan Kabul.

Mafi yawansu, sun rasa iyayen su ne sakamakon yakin basasar da aka dade ana tafkawa akasar.

Yaran kan yi kokarin goge gilasan mota a kan titunan birnin domin samun na abinci.

Yaran da ya kamata su kasance a makaranta, sun bige da koyan bara a kan tituna.

"A kullum adadin yaran da ke bara karuwa yake yi, saboda 'yan gudun hijira na dawowa daga Iran da Pakistan, sannan jama'a na kara gujewa yakin da ake ci gaba da tafkawa," inji Muhammad Yousuf, wanda ke fafutukar samawa yaran matsuguni.

Ya kara da cewa idan suka girma ba za su fahimci wani abu mai mahimmanci ba, saboda tunanin su ya riga ya gurbata.

Image caption Har yanzu akwai yaran da suke samun damar halattar makaranta

Shaye-shaye

Adadin masu shaye-shaye na kara karuwa, alkaluman baya-bayannan sun nuna cewa akwai akalla mutane miliyan daya da rabi, mafi yawansu yara kanana ne.

Cikin su harda dan shekara 13 Omid, duk da cewa ya musanta amma idanuwan sa sun zayyana ainahin halayyar sa.

Sai dai ba duka aka taru aka zama daya ba, akwai yaran da ke samun damar zuwa makaranta.

Aschiana, na daya daga cikin kungiyoyin da ke taimakawa yara, domin hada ayyukan kan hanya da karatu.

Nargis na daya daga cikin irin wadannan yara, tana zama a gaban waji dogon benci tsakanin yara 'yan uwanta.

Image caption Mahfouz yana wanke mota a gefen titin birnin Kabul

Iyayen da suka yi kaura

Mahfouz ya dade yana aiki tun yana dan shekara bakwai. Baban sa ya kauracewa babar sa tun tuni, abinda yasa shi kadai ne ke fafutuka.

Yace: " ya sanya rayuwar mu a cikin hadari, talakawa ne mu, don haka dole na ta shi domin sama mana kalaci".

Wurin da yake zuwa na gab da inda aka kai harin kunar bakin wake na kwanan nan, sai dai yace ba ya tsoran komai yanzu.

Nargis ta nuna damuwa kan yadda mahaifinta ya watsar da su tare da babar su, sai dai tana fatan abubuwa za su dai dai ta nan gaba.

A yanzu dai akwai dubban yara da ke dandana kunar da yakin da aka shafe shekara da shekaru ana gwabzawa a kasar ya haifar.