EFCC za ta fara binciken kadarorin jama'a

Taswirar Najeriya
Image caption Najeriya ta yi kaurin suna wajen cin hanci da rashawa da halatta kudin haram

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arziki ta'annati EFCC, ta kafa wata tawagar bincike da za ta binciki tushen kadarorin da ba'a hakikance yadda aka same su ba a Nijeriya.

Wannan taw

aga a fadin hukumar ta EFCC na wani bangare ne a fafutukar da take yi na yaki da almundahana da kuma yaki da dabi'ar nan ta tsaftace kudaden haram.

Shugabar hukumar Misis Farida Waziri da ta bayyana hakan, tace wannan tawagar masu bincike za ta rinka fita aiki akai-akai domin binciko tushen dukiyar da aka yi amfani da ita wajen mallakar wasu kaddarori.

Musamman wadanda masu su basu iya fayyace yadda suka sami wannan dukiya ba.

Misis waziri tace idan kuwa ta tabbata cewa da akwai ayar tambaya kan dukiyar to fa kwace kadarorin hukumar ta EFCC za ta yi, ta mika su ga gwamnatin tarayya.

Tanadin doka

Ko da yake doka ta baiwa hukumar EFCC ikon bincike kan dukiya da kadarar da wani dan kasa ya mallaka wanda a ganin hukumar akwai shakku game da yadda ya mallaki dukiyar.

Wasu 'yan kasar na fargabar cewa mai yiwuwa hakan ya bayar da kafa ga masu rike da madafun iko su takura ko musgunawa 'yan hamayya, ganin yadda zabe ke kara karatowa.

Sai dai a hiyarsa da BBC, mai magana da yawun hukumar ta EFCC Femi Babafemi, ya kawar da wannan fargaba.

Yace ba ni ganin wani abin damuwa tattare da wannan, saboda matakin ba shi da nasaba da siyasa ko kuma zabe.

Ganin cewa gane haramci ko akasin haka kan dukiya abune mai wahala, amma Femi Babafemi ya ce suna da nasu dabarun.

"za mu iya gayyatar wadanda muke da shakka kan shi ya bayyana mana ta yadda yake samun kudin sa da kuma irin ayyukan da ya saka a gaba".

Gabannin wannan sabon matakin dai, hukumar EFCC ta gabatar wa da majalisar kasa daftarin dokar da zai baiwa EFCCn damar kwace dukiya ko kadarorin da wani ya mallaka ta haramtacciyar hanya, amma dokar ta fuskanci koma baya a majalisar.