Jamaica ta sha alwashin maido doka da oda

Rikicin Jamaica
Image caption Hayaki ya turnuke sararin samaniyar Kingston babban birnin Jamaica

Pira ministan kasar Jamaica Bruce Golding ya sha alwashin maido da doka da oda a kasar bayan mutane 31 sun mutu sakamakon rikicin da jami'an tsaro suke yi da masu safarar kwayoyi.

Pira ministan ya ce, ya yi nadamar rasa rayukan da aka yi. Sai dai ya ce, 'yan sanda za su ci gaba da binciko makaman da aka mallaka ba bisa ka'ida ba, da kuma mutanen da ake zargi da aikata laifuka.

Mutanen dai sun rasa rayukansu ne sakamakon artabun da jami'an tsaron kasar ke yi da 'yan bindiga a wani yunkurin karbe ikon unguwar da mutumin da ake zargin rikakken mai safarar miyagun kwayoyi ne wato Christopher Coke ke zaune.

Tashin hankali ya kazanta ne a Kingston babban birnin kasar, yayinda 'yan sanda suka shiga wani yanki na birnin dake karkashin Christopher Dudas Coke.

Gwamnatin Amurka dai tana fatan a tesa keyar Mr Coke din don ya fuskanci shari'a a birnin New York bisa zargin fataucin miyagun kwayoyi.

Kwana daya bayan saka dokar hana yawo a Kingston, har yanzu ana cigaba da zub da jini da majina a tsakanin 'yan sanda da magoya bayan wanda ake zargi da kasancewa shugaban masu harka da kwaya.

Cikin dare an yi ta jin karar harbe harbe a babban birnin na Jamaica, kuma tashin hankalin ya raja'a ne a wani bangaren garin da ake cewa Tivoli Gardens, kuma nan ce matattarar da Christopher Coke wanda aka fi sani da suna Dudas yake.

Wakilin BBC Mathew Price wanda ke bin diddigin labarin: "Yace cikin dare an ci gaba da fadan da ake yi a tsakanin dakarun gwamnati wato 'yan sanda da kuma masu dauke da bindiga wadanda ke biyayya ga Christopher Coke.

Ya kara da cewa ina ga dai yana da mahimmanci a fahimci cewa ba wai a duk babban birnin Jamaican wato Kingston ake fadan ba, a wadansu kebabbun wurare ne.

Image caption Jami'ain tsaron Jamaica na ci gaba da artabu da yan bindiga

Wadanda abin ya ritsa da su

Mutane da yawa sun jikkata. Dakarun gwamnati na ta kira kan kawo taimako ga 'yan uwansu da suka ji rauni a sanadiyar fafatawa da magoya bayan Mista Coke.

Akwai dai wadansu rahotanni da ba a tabbatar da su ba dake cewa harma da al'ummar farar hula.

Kuma dai tabbas wuri ne da al'ummar wani gari mai suna Garrison suke wadanda rikicin ya rutsa dasu.

Da yawa dai na ganin cewa Mr. Coke ya kula dasu a lokacin da gwamnati ta yi watsi dasu.

Kawo yanzu dai babu alamar cewa jami'an tsaro sun yi nasara wajen kame wanda suke nema.

Aikin sam ba mai sauki bane gare su yayin da magoya bayan Mr. Coke ke dauke da muggan makamai.

Mace-Mace

Akalla fararen hula ashirin da shida ne suka rasa rayukansu, yayinda jami'in soji daya shi ma ya mutu.

An kuma kama mutane 211, ciki har da mata shida, sai dai babu tabbacin cewa Mr. Coke na cikinsu.

Sojoji da 'yan sanda sun fara binciken gida-gida suna neman Mr. Coke, wanda ake nemansa a Amurka bisa zargin safarar makamai.

Idan aka kama shi dai, Mr. Coke na fuskantar hukuncin daurin rai da rai a karar da aka shigar kansa a birnin New York na Amurka.

Harkar safarar miyagun kwayoyi dai ta yi tsamari a kasar ta Jamaica, tsibirin da yake da al'umma kimanin miliyan uku.