Mutane uku sun halaka a Kasar jamaica

Rikicin Jamaica
Image caption Hayaki ya turnuke sararin samaniyar Kingston babban birnin Jamaica

Mutane uku ne suka halaka a Jamaica sakamakon artabun da jami'an tsaron kasar keyi da 'yan bindiga a yunkurin karbe ikon unguwar da rikakken mai safarar miyagun kwayoyi Christopher Coke ke zaune.

Tashin hankali ya kazanta ne a Kingston babban birnin kasar, yayinda 'yan sanda suka shiga wani yanki na birnin dake karkashin Christopher Dudas Coke.

Gwamnatin Amurka dai tana fatan a tesa keyar Mr Coke din don ya fuskanci shari'a a birnin New York bisa zargin fataucin miyagun kwayoyi.

Kwana daya bayan saka dokar hana yawo a Kingston, har yanzu ana cigaba da zub da jini da majina a tsakanin 'yan sanda da magoya bayan wanda ake zargi da kasancewa shugaban masu harka da kwaya.

Cikin dare an yi ta jin karar harbe harbe a babban birnin na Jamaica, kuma tashin hankalin ya raja'a ne a wani bangaren garin da ake cewa Tivoli Gardens, kuma nan ce matattarar da Christopher Coke wanda aka fi sani da suna Dudas yake.

Wakilin BBC Mathew Price wanda ke bin diddigin labarin: "Yace cikin dare an ci gaba da fadan da ake yi a tsakanin dakarun gwamnati wato 'yan sanda da kuma masu dauke da bindiga wadanda ke biyayya ga Christopher Coke.

Ya kara da cewa ina ga dai yana da mahimmanci a fahimci cewa ba wai a duk babban birnin Jamaican wato Kingston ake fadan ba, a wadansu kebabbun wurare ne.

Image caption Jami'ain tsaron Jamaica na ci gaba da artabu da yan bindiga

Wadanda abin ya ritsa da su

Mutane da yawa sun jikkata. Dakarun gwamnati na ta kira kan kawo taimako ga 'yan uwansu da suka ji rauni a sanadiyar fafatawa da magoya bayan Mista Coke.

Akwai dai wadansu rahotanni da ba a tabbatar da su ba dake cewa harma da al'ummar farar hula.

Kuma dai tabbas wuri ne da al'ummar wani gari mai suna Garrison suke wadanda rikicin ya rutsa dasu.

Da yawa dai na ganin cewa Mr. Coke ya kula dasu a lokacin da gwamnati ta yi watsi dasu.

Kawo yanzu dai babu alamar cewa jami'an tsaro sun yi nasara wajen kame wanda suke nema.

Aikin sam ba mai sauki bane gare su yayin da magoya bayan Mr. Coke ke dauke da manyan makamai.