Najeriya za ta fadada hanyoyin samun kudaden shiga

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Shugaban Nijeria, Dr Goodluck Jonathan ya ce abin takaici ne yadda Najeriya ta zama wata kasa da ta kusan dogara kacokan a kan hanya daya wajen samun kudaden shiga.

Da yake bude wata masana'antar sarrafa ma'adinai da ake hakowa daga kasa a jahar Zamfara dake arewacin kasar, Shugaba Jonathan ya ce harkokin noma da hakar ma'adinai wadanda Najeriya ta dogara a kansu wajen samun kudaden shiga kafin a gano danyen mai, yanzu kusan sun durkushe ga baki daya.

Wannan dai ita ce ziyara ta uku da ya kai a wata jaha a kasar tun bayan zama shugaban kasa a farkon wannan watan.

Shugaba Goodluck Jonathan ya ce kafin yakin basasa kasar a karshen shekarun alif dari tara da sittin dai harkokin noma da hakar ma’adinai su ne manyan hanyoyin samun kudaden shiga a kasar, amma yace yanzu kan an yi watsi da wadannan fannonin.

Yace yanzu kan Najeriya ta zama kasar da ta kusan dogara akan hanya daya wajen samun kudaden shiga wannan abin takaici ne in ji shi saboda a zahiri take cewa muna iya kara samun arzikin kasa ta hanyar aikin gona da kuma hakar ma’adinai.

"Kakannin mu sun gaya mana cewar Najeriya tayi yakin basasa na shekaru tana amfani da kudaden da ake samu daga noma kuma ba tare da neman aron ko da taro ba daga wata kasa ba, amma yanzu fannonin noma da hakar ma’adinan duk sun mutu", in ji Jonatahan.

"Saboda haka wannan gwamnatin ke kokarin yawaita hanyoyin bunkasar tattalin arzikinta ta hanya raya harkar noma da kiwo na kasuwanci da kuma ta haka da kuma sarrafa ma’adinai"

Gwamnan jahar ta Zamfara Mahmuda Aliyu Shinkafi ya ce Gwamtin jihar ta gina masana’antar ne tare da hadin gwiwar wani kanfani na kasar Sin bisa kudi kimanin Naira biliyan huda daidai da miliyan ashirin da takwas na dalar Amurka.

"Bukatar mu ita ce mu hako kuma mu sarrafa wadannan dimbim ma’adinai da muke dasu domin bunkasa tattalin arzikin jahar nan don samun karin hanyoyin samun kudaden shiga, samar da ayyukan yi da rage fatara tsakanin jama’armu, in ji Mamuda Aliyu.

Sai dai wasu lokuttan gwamnatoci a kasar sukan narkar da kudade wajen aiwatar da ire-iren wadannan ayyukkan, amma daga bisani sai a yi watsi da su. Sai dai gwaman ya ce "Ina son shaida wa shugaban kasa cewar da zarar aka kaddamarda wannan masana’antar to za’a soma sarrafa wasu ma’adinai, kuma da yardar Allah za’a fara aike wa da danyar hajar da za ta samar zuwa kasashen waje a cikin wata daya.

Kafin wadannan jawaban dai shugaban ya kalli raye-rayen gargajiya na manyan kabilun kasar da kuma na jahar da ya fito wato Bayelsa da suka zo yi masa maraba.