An mai da wa Ribadu Mukaminsa

Nuhu Ribadu
Image caption Tsohon Shugaban hukumar EFCC a Najeriya

A Najeriya, Hukumar da ke kula da ayyukan `yansan kasar ta sake mayar wa tsohon shugaban Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Mallam Nuhu Ribadu mukaminsa na mataimakin sepeta-janar din `yan sanda.

Kazalika Hukumar ta sauya matakin da ta dauka na korarsa daga aikin dan sanda zuwa ritaya. Hukumar ya yanke wannan sabon hukuncin ne a wani zaman da ta yi jiya.

A shekara ta dubu biyu da takwas ne Hukumar ta rage wa Mallam Ribado mukami daga mataimakin sepeta-janar zuwa mataimakin kwamishinan `yan sanda bisa zargin cewa ba a bi ka`ida ba wajen ciyar da shi gaba.

Bayan wani zaman da ta yi Hukumar da ke kula da ayyukan `yan sandan Najeriyar ta yi amai ta lashe, inda ta warware tsohon hukuncin da ta yi a shekara ta 2008 na rage wa tsohon shugaban Hukumar nan da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa, wato EFCC, Mallam Nuhu Ribado mukami daga mataimakin sepeta-janar zuwa mataimakin Kwamishinan `yan sanda.

Mai magana da yawun hukumar

Mr Ferdinand Ekpe Kakakin Hukumar Kula da Ayyukan `yan sandan, ya ce; "Hukumar ta yi zama jiya kuma ta mai da shi bakin aiki tare da yi masa ritaya a matsayin mataimakin sepeta janar na `yan sanda, inda ritayar ta fara daga shekara ta 2008".

Wakilin BBC ya tambaye shi ko da wasu sharuda tattare da ritayar da aka yi wa jami`in? sai ya ce "idan ka yi ritaya a aikin gwamnati ka cancanci duk wata alfarmar da ake yi wa duk wanda ya kai mukaminka. Don haka shi ma ritaya ya yi ya cancanci duk wata alfarma ko karamci da akan yi wa wanda ya yi ritaya a mukaminsa".

Wannan hukumar dai ita ce ta yi tsohon hukuncin shekaru biyu da suka wuce, yanzu kuma sai ga shi ta yi amai ta lashe.

Ko da yake rahotanni na nuna cewa ba haka kawai Hukumar ta sauya matsayin nata rana-tsaka ba sai da ta fuskanci matsin lamba daga mahukuntan kasar. Amma kakakin ba haka maganar take ba.

Ya ba ni da labarin cewa Hukumar ta mika wuya ga wani . Amma ka san cewa yana daga cikin ikon Hukumar kula da ayyukan `yan sanda ta dauki ma`aikata ko ciyar da su gaba ko kuma ladabtar da su.

Kuma a koda yaushe aka kai mata kuka ko da ta yanke wani hukunci na ladabtarwa tana da `yancin sake dubawa tare da sauya matsayi. To a bin da ya faru da wannan ke nan. Jami`in da ake maganar ne ya nemi a masa hakan.

Wakilin BBC ya yi kokarin tuntubar Lauyan Mallam Nuhu Ribadon, Femi Falana ta wayar tarho don jin nasu martanin dagane da wannan mataki da hukumar kula da ayyukan `yan sandan ta dauka amma ban yi nasara ba.

Karin mukami

Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ne dai ya yi wa mallam Nuhu Ribado karin mukami zuwa mataimakin sepeta janar na `yan sanda.

Amma a watan Agustan shekara ta 2008 sai hukumar da ke Kula da ayyukan `yan sandan ta rage wa mallam Nuhu Ribado mukami, tare da wasu jami`an `yan sanda dari da talatin da tara bisa hujjar cewa an yi musu karin makamin da ya saba da ka`ida.

Daga bisani ta kore shi daga aikin dan sanda a watan Disamban shekara ta 2008.

Abin da hukumar ba ta fito ta yi bayaninsa shi ne makomar sauran jami`ai 139 da ta rage wa mukami tare da Mallam Nuhu Ribadon a shekara ta 2008 din.