Clinton ta gargadi Koriya ta Arewa da ta daina neman fada

Hillary Clinton
Image caption Hillary Clinton Sakatariyar harkokin wajen Amurka

Sakatariyar harkokin wajen Amruka Hillary Clinton ta yi kira ga Koriya ta Arewa da ta daina barazana da tsokana saboda nutsewar jirgin ruwan yakin Koriya ta Kudu.

Lokacin da take jawabi a birnin Seoul Mrs Clinton tace akwai hujjojin da suke nuna cewa Koriya ta Arewa ce ta nutsar da wannan jirgi, kuma hakan yana bukatar mayar da martanin da ya dace da kasashen duniya.

Hillary Clinton ta ce, makomar Koriya ta Arewa za ta danganta ne da irin zabin da shugabanninta suka yi a yanzu.

Sai dai Koriya ta Arewa ta mayar da nata martanin, wanda a cikinsa wani tsohon gwarzon sojan Koriya ta arewa, Manjo Janar Pak Chan Su, ya ce makiyansu na amfani da batun nutsewar jirgin ruwan koriya ta kudu domin neman a saka masu takunkumi.

Ya ce, amma suma za su mayar da martani, ba za su amince da tsokana daga makiyansu ba.