Nakasassu sun yi zanga zanga a Abuja

Sandar Guragu
Image caption Sandar Guragu

Kungiyoyin nakasassu daga bangarori da dama na Najeriya sun gudanar da wani gangami domin nuna rashin jin dadinsu ga majalisar dokoki ta kasa bisa abin da suka ce rashin sanya su a cikin tsarin tafiyar da mulki a Najeriya. Kungiyoyin nakasassun sun yi kira da majalisa dokokin ta hanzarta kammala aikin da ta ke yi kan kudurin da zai basu damar samu hukumar da zata rinka kulawa da su.

Sun kuma yi barazanar cewa kin yin hakan zai tilasta musu buga sunayen 'yan majalisar da suke zargin na yin katsalandan wajen tabbatar da 'yancin nasu a kafafen yada labarai na kasar domin jama'a su gani.

Ba tun yau ne dai ba kungiyoyin nakasassun suke wannan fafutika ta neman a dama da su a al'amuran kasar.