Indonesia ta kulla yarjejeniya tare da Norway kan sarar daji

Gandun dajin Indonesia
Image caption Gandun dajin Indonesia

Gwamnatin Indonesia ta ce ta sa hannu akan wata yarjajeniya tare da kasar Norway, wadda a karkashinta, Indonesiyar za ta daina sare dazuzuka da kuma kone su har tsawon shekaru biyu.

A maimakon haka, Norway ta yi, alkawarin baiwa Indonesiyar taimakon fiye da dala biliyan guda, domin gudanar da shirye-shirye na kare dazuka.

Indonesiya na daga cikin kasashen duniyar da suka fi samar da iskar da ke gurbata muhalli, kuma ita ce ke kan gaba a duniya, wajen sare dazuka. Bincike ya nuna cewa, a kowace awa guda, ana sarar dazukan da fadinsu ya kai filayen kwallon kafa dari ukku, a Indonesiyar.

Wani jami'in wata kungiyar kare muhalli,ya ce sau da yawa za ka ga an ba kamfanoni izinin sharar gonaki a dazukan Indonesia,to amma kawai sai su sassare itatuwa, su yi batan-dabo.