Yajin aikin masu amfani da wayar salula a Ghana

Taswirar kasar Ghana
Image caption Ghana na daga cikin kasahen da ake amfani da wayar salula sosai a Afrika

Hukumar kare hakkin masu sayen kaya a Ghana (CPA), ta nemi masu amfani da wayar salula a kasar, da su kashe wayoyin su har na tsawon sa'o'i shida.

Hukumar na son ganin anyi hakanne a safiyar ranar Alhamis, domin nuna adawa da rashin kyawun layukan sadarwa a kasar.

Hukumar na bukatar a rage kudaden da kamfanoni ke karba, da tallace-tallace marasa amfani da kuma habaka ingancin sadarwar baki daya.

Har ila yau hukumar ta yi kira da a gudanar da zanga zanga a babban birnin kasar Accra.

Amma wakilin BBC a birnin Acrra, Iddi Ali, yace jama'a basu fito sosai domin halattar wannan zanga zangar ba.

Banbancin ra'ayi

Wasu mazauna birnin Accra da suka zanta da BBC sun ce su ba za su kashe wayoyin su ba, saboda basu ga mahimmancin yin hakan a gare su ba.

Yayinda wasu kuma suka ce sun goyi bayan matakin domin neman 'yan cinsu.

Hukumar ta ce yajin aikin masu amfani da wayar zai haifar da asarar dala miliyan shida ga kamfanonin.

Kuma tana saran hakan zai tilastawa kamfanonin sadarwa a kasar kimanta masu amfani da kayan na su.